Nijar (ƙasa)
Appearance
| |||
Yaren kasa | Hausa, Zarma, Fulfulde, Tamasheq, Larabci, da sauransu | ||
baban birni | Niamey | ||
shugaba | Issoufou Mahamadou | ||
firaminista | Birgini Rafini | ||
fadin kasa - % ruwa |
1,267,000 km² | .02% | ||
yawan mutanen kasa - a gidayar(2013) - wurin zaman mutane |
17 129 076 9,2/km² | ||
Kudin da yake shiga kasa a kowace ( shekara) - |
$11.82 billion | ||
Kudin da kowane mutum yake samu a shekara | $900 | ||
Kudin kasa | CFA frank | ||
Banbanci lokaci | +1 (UTC) | ||
Rane | +1 (UTC) | ||
Samun 'yancin kasa daga Faransa | 3 Augustus 1960, | ||
Yadda ake kiran mutanen kasar | 'yan Nijar | ||
Lambar yanar gizo | .ne | ||
lambar wayar tarhon | +227 |
Kasar Nijar tana daya daga cikin kasashan Afrika ta yamma. Tana makwabtaka da kasashe bakwai ( Nijeriya, Libya, Aljeriya, Mali, Burkina Faso, Benin, Cadi. Tana da al'umma da ta kai fiye da mutum miliyan 12. Kuma tana da kabilu 8. Su ne: Hausawa, Zabarmawa, Fulani, Bugaje, Barebari, Larabawa, Tubawa, da Gurmawa.
Nijar ta samu 'yancin kan ta a shekarar 1960 daga Turawan mulkin mallaka na Faransa.
Al'Ummar Nijar
A lissafin kasafin kasa da INS ta fitar (http://www.stat-niger.org/statistique/), a shekarar 2013 kasar Nijar ta na da al'umma 17 129 076.