Jump to content

Christian Chukwu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Christian Chukwu
mutum
Bayanai
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Country for sport (en) Fassara Najeriya
Suna Christian
Sunan dangi Chukwu
Shekarun haihuwa 4 ga Janairu, 1951
Yaren haihuwa Harshen, Ibo
Harsuna Turanci, Harshen, Ibo da Pidgin na Najeriya
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa da association football manager (en) Fassara
Matsayin daya buga/kware a ƙungiya Mai buga baya
Mamba na ƙungiyar wasanni Enugu Rangers da Ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Najeriya
Wasa ƙwallon ƙafa
Participant in (en) Fassara 1978 African Cup of Nations (en) Fassara da 1980 African Cup of Nations (en) Fassara

Christian Chukwu (an haife shi ranar 4 ga watan Janairun shekarar 1951[1]) tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Najeriya kuma tsohon kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasa. Ɗan wasan baya a lokacin wasansa, ya zama kaftin ɗin tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya zuwa nasarar farko a gasar cin kofin ƙasashen Afrika.

Sana'ar wasa

[gyara sashe | gyara masomin]

A matsayinsa na ɗan wasa, ya zama kaftin ɗin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Enugu Rangers da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya a ƙarshen shekarun 1970. Shi ne kaftin ɗin Najeriya na farko da ya ɗauki kofin gasar cin kofin Nahiyar Afrika bayan da suka doke Algeria da ci 3-0 a wasan ƙarshe na gasar 1980.[2]

Aikin koyarwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Chukwu ya fara aikin horaswa ne a ƙasar Lebanon a tsakiyar shekarun 1990, kafin a naɗa shi kocin tawagar ƙasar Kenya a shekarar 1998. Daga baya, daga shekarar 2003 zuwa 2005, ya horar da Najeriya, inda ya kai su wasan dab da na kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin Afrika ta shekarar 2004. A lokacin wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a shekara ta 2006, an zargi Chukwu da rashin horarwa da gudanar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, kuma an dakatar da shi wasanni biyu kafin a kammala kamfen ɗin shiga gasar.[3] A karawa biyu gida da waje - da Angola wadda ta yi nasara a rukunin, Najeriya ta kasa lashe ko ɗaya daga cikin karawa biyun. An ɗora alhakin hakan kan Chukwu kuma waɗancan manyan gazawar biyu sun kai ga kasa samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya, bayan da ta fito a duk wasannin da ta buga a gasar cin kofin duniya tun bayan da ta fara wasa a cikin shekarar 1994.

Chukwu ya horar da Enugu Rangers zuwa matsayi na 6 a gasar Premier ta Najeriya a shekarar 2008 zuwa 2009. Duk da haka, an kore shi a ranar 5 ga watan Agustan 2009 saboda ya kasa cimma burin ƙungiyar a kakar wasa ta bana.

Daga baya rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin watan Afrilun 2019 ne hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya ta sanar da cewa za ta taimaka wa Chukwu ya biya kuɗin jinya a Amurka,[4] yayin da hamshaƙin attajirin nan Femi Otedola ya ce shi ma zai bayar da gudunmawarsa.[5] Daga baya aka sanar da cewa zai je neman magani a cikin watan Mayu bayan an tara kuɗaɗen da ake buƙata ya warke.[6]

  1. "Christian CHUKWU". FIFA. Archived from the original on 15 February 2009. Retrieved 2009-10-16.
  2. "African Nations Cup 1980". 2003-05-01. Retrieved 2009-10-16.
  3. "Nigeria suspends Chukwu". BBC Sport. 21 June 2005.
  4. "Nigeria Football Federation to help ailing legend Christian Chukwu". BBC Sport. 8 April 2019.
  5. "Billionaire Femi Otedola to cover costs for ailing legend Christian Chukwu". BBC Sport. 9 April 2019.
  6. "Chukwu to travel for treatment in May". BBC Sport. 24 April 2019.