Danielle Steel
Danielle Fernandes Dominique Schuelein-Steel (an haifeta a watan Agusta 14, 1947) marubuciya ce Ba'amurkiya wacce aka fi sani da littattafan soyayya. Ita ce fitacciyar marubuciya mai raye-raye kuma ɗaya daga cikin mafi kyawun marubutan almara na kowane lokaci[1], tare da sayar da kwafi sama da miliyan 800.[2] Tun daga 2021, ta rubuta littattafai 190, gami da litattafai sama da 140[3].
Da tasowarta a California inda mafi yawan karioyarta tasoma, Steel ta samar da littattafai da yawa a shekara, galibi tana gwamutsa har zuwa ayyuka biyar lokaci guda. Duk litattafanta sun kasance masu siyarwane matuqa, gami da waɗanda aka fitar a cikin hardback, duk da "rashin yabo mai yawa" (Makonnin Mawallafa).[4] Littattafanta galibi suna haɗawa da iyalai masu arziki da ke fuskantar matsala, waɗanda abubuwa masu duhu kamar kurkuku, zamba, cin zarafi da kisan kansa ke barazana. Steel ta kuma buga labarin almara da waqoqin yara, da kuma samar da wata gidauniya da ke ba da tallafi ga kungiyoyi masu alaka da tabin hankali[5]. An fassara littattafanta zuwa harsuna 43,[6] tare da 22 da aka daidaita don talabijin, gami da biyu waɗanda suka karɓi zaɓin Golden Globe.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://en.wikipedia.org/wiki/List_of_best-selling_fiction_authors
- ↑ https://www.forbes.com/profile/danielle-steel/?sh=4cf1ea109edd
- ↑ https://www.instyle.com/fashion/danielle-steels-wardrobe-home-tour
- ↑ https://www.publishersweekly.com/978-0-312-11257-8
- ↑ http://nicktrainafoundation.com/
- ↑ https://daniellesteel.com/about-danielle/