Jump to content

Jamila Nagudu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jamila Nagudu
Rayuwa
Haihuwa 10 ga Augusta, 1985 (39 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan wasan kwaikwayo da jarumi
Jamila Umar Nagudu
jamila Umar Nagudu

Jamila Umar Nagudu[1] (an haifeta a ranar 10 ga watan Agusta, a shekarata alif ɗari tara da tamanin da biyar 1985). wacce aka fi sani da Jamila nagudu, ƴar wasan Kannywood ce ta Najeriya.[2][3]Jarumar ta yi fina -finai da dama irin su Indon ƙauye 2

Jamila da Jamilu

Tutar So

Matar Aure

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Jamila Nagudu a ranar 10 ga Agustan shekarar 1985 a cikin garin Magana Gumau, ƙaramar hukumar Toro a jihar Bauchi, Najeriya . Jamila ta yi makarantun firamare da sakandare a jihar Bauchi.[ana buƙatar hujja]

Jamila Umar wacce aka fi sani da Jamila Umar Nagudu ta fara fitowa a masana’antar Kannywood a shekara ta 2002. Tun lokacin da ta rabu, ta yanke shawarar fara fim. Ta bar Bauchi ta koma Kano ta gane cewa ta cimma burinta na zama jarumar fina-finai a masana'antar Kannywood. Ta kasance a harkar fim a matsayin mai rawa tun (a shekarar 2002). Sannan daga baya ta shiga harkar fim kaɗan kaɗan. Ƙoƙarin da ta yi a harkar nishadantarwa da wasan kwaikwayo ya jawo hankalin daraktoci har suka fara nuna ta a cikin fina-finansu. Jamila na iya fitowa a kowace rawa. Ta fito a fina-finan soyayya amma wani lokacin ma tana fitowa a fina-finan barkwanci. Nagudu ta yi fice sosai a Kannywood ta yadda ake yi mata lakabi da "Sarauniyar Kannywood". Darakta Aminu Saira shi ne ya fara jefa ta a fim din "Jamila da Jamilu" a matsayin jaruma.[4] An zaɓe ta a matsayin mafi kyawun Nollywood a Abeokuta.[5]

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Jalima ta rabu da mijinta kuma tana da ɗa.[6][7] yaron ta a yanzu haka ya zama matashin saurayi, tayi aure da dama amma a yanzu haka bata da aure.

  1. https://kannywoodsceneblog.wordpress.com/tag/jamila-nagudu/
  2. "Tarihin Jaruma Jamila Umar Nagudu (Jamila Nagudu)". Haskenews-All About Arewa. Retrieved 2022-03-25.
  3. Adeleye, Kunle (2021-12-25). "Meet The Queen Of Kannywood, Jamila Umar Nagudu: Full Biography". Glamsquad Magazine (in Turanci). Retrieved 2022-03-25.
  4. "'Ibada da fim ne suka fi muhimmanci a wurina'". BBC News Hausa. 2018-04-04. Retrieved 2022-03-25.
  5. Online, Tribune (2017-09-16). "BON Awards: Jamila Nagudu, Omotola, others get nominations". Tribune Online (in Turanci). Retrieved 2022-07-28.
  6. "Ba ni da saurayi a Kannywood — Jamila Nagudu". BBC News Hausa. Retrieved 2022-03-25.
  7. "Opera News Detail". lucky-wap-ams.op-mobile.opera.com. Retrieved 2022-03-25.