Jump to content

User:Ammarpad

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ina maku barka da zuwa shafina. Nine Ammarpad, ni cikakken Bahaushe ne kuma ɗaya daga cikin editocin Wikipedia. A kodayaushe ina alfahari da nuna ma mutane alfanun sa kai domin inganta muƙalolin Wikipedia ta harshen Hausa domin ci gaban ilimi da ma ƙara yaɗuwar harshen Hausa a faɗin duniya. Gyaran Wikipedia (ƙirkiro sabbin muƙaloli ko kuma inganta waɗanda ke akwai) bashi da wahala, amma kuma amfanin hakan baya misaltuwa.

Domin haɓaka wannan manhaja, na shirya taron Hausa Wikipedia a Kano a shekarar 2018 wanda shine taron farko akan hakan a duk faɗin Arewacin Najeriya. Daga nan an shirya wasu tarukka ba adadi a wurare daban daban na sassan Najeriya.

Idan kai bahaushe ne ko ke bahaushiya ce, ina gayyatar ku mu inganta wannan rumbun ilimin. Idan kuna buƙatar ƙarin bayani, shawara ko ƙarin haske a kan Hausa Wikipedia ko yadda zaku bada gudummuwa, zaku iya tambaya ta a nan ko kuma ku tura man saƙon email ta ammar(_AT_)wikimediahausa.org domin tattaunawa sosai.

Har ila yau, ina kuma da wani account wanda yake aiki da kanshi (wato robot), amma fa yana jin Hausa kamar jakin Kano. Zaku iya ganin ayyukan shi a nan: AmmarBot.

Harsunan edita
ha-N Wannan edita cikakken Bahaushe ne.
en-4 This user has near native speaker knowledge of English.
fr-3 Cet utilisateur dispose de connaissances avancées en français.
Editoci da yarensu